A cewar gidan rediyon WDR, wanda ya aikata laifin wani matashi ne dan garin Hamm, ya kuma afakawa dalibai ne da wuka a cikin wani gini na taron karawa juna sani a yau Juma'a a jami'ar Hamm-Lippstadt da ke North Rhine-Westphalia a kudancin Jamus.
A wani lamari na daban, wata mata da wata yarinya ‘yar shekara bakwai sun samu munanan raunuka sakamakon harin wuka da aka kai a wata makarantar firamare da ke Esslingen da ke kusa da Stuttgart.
Jamus ta kadu a farkon wannan shekarar sakamakon hare-hare a makarantu da ba kasafai ake ganin irinsa ba, bayan da wani dalibi dan shekara 18 ya bude wuta a wani dakin karatu na jami'ar Heidelberg da ke kudu maso yammacin kasar, inda ya kashe wata budurwa tare da raunata wasu uku kafin ya tsere.