Shugaba Gotabaya Rajapaksa na kasar Siri Lanka ya rantsar da Ranil Wickremesinghe mai shekaru 73 da haihuwa a matsayin sabon firaministan kasar. Tuni shugaban kasar ya bukaci 'yan adawa da jami'an gwamnatinsa bisa aiki tare kan samar da mafita bisa yanayin da kasar take ciki na matsalolin tattalin arziki.
Sabon firamnistan ya kadance gogeggen dan adawa wanda yake rike mukamun sau biyar, kuma sabuwar gwamnatin da Firaminista Ranil Wickremesinghe zai jagoranta tana da jan aikin farfado da tattalin arzikin kasar.
Nadin ya zo kwanaki uku bayan Firamnista Mahinda Rajapaksa dan-uwan Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya ajiye aiki sakamkon zanga-zanga kan tabarbarewar tattalin arziki da kasar ta Siri Lanka ta samu kanta a ciki.
Tashe-tashen hankula da suka biyo zanga-zangar neman gwamnatin kasar ta yi murabus sun janyo mutuwar mutane tara yayin da wasu kimanin 300 suka jikata.