Sabon shugaban kasar Lebanon Joseph Aoun ya nada Nawaf Salam a matsayin sabon firaminista a yau Litinin, tare da dora masa nauyin tunkarar manyan kalubalen da kasar ke fama da su a shekarun baya-bayan nan.
Shi dai Nawaf Salam mai shekaru 71 a duniya ya kasance gogaggen jami'in diflomasiyya kuma yana rike da mukamin shugaban kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ICJ da ke birnin Hage na kasar Netherland, kafin a nada shi a matsayin firaminista.
Takararsa a kan wannan mukami ta samu goyon bayan jam'iyyu masu adawa da kungiyar Hezbollah mai alaka da Iran wadda ta samu gagarumin koma-baya bayan yakin da ta gwabza da Isra'ila a baya-bayan nan.
Ana dai kallon Nawaf Salam a matsayin mutum mai ilimi da ka iya taka rawar gani a Lebanon, kuma ana sa ran zai isa kasar a gobe Talata domin kafa sabuwar gwamnati.