Shugabanin kasashen gabashi da kudanci da ma yammacin Afirka ne suka yi nadin a wani yunkuri na kawo karshen yakin basasa a gabashin Kwango, tare da cimma matsaya kan batun yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakanin 'yan tawaye da gwamnatin Kinshasa ke zargi na samun goyon bayan Rwanda da hukumomi na gwamnatin tsakiya.
Wasu daga cikin tsofaffin shuwagabannin kasashen sun hada da Uhuru Kenyatta na kasar Kenya da Hailemariam Desaleg na kasar Habasha da kuma tsohon shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Najeriya
Har yanzu kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afirka ta AU sun gaza shawo kan rikicin na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon wanda ya lakume rayuwakn fararen hula da dama.