An kori ministan Senegal

Cheikh Oumar Diagne minista mai kula da harkokin mulki a fadar shugaban kasar ya furta kalaman lokacin hira da wata tashar talabijin ta kasar. Tuni aka maye gurbin korarren ministan da Papa Thione Dieng karkashin okar da shugaban kasar ya fitar.

Karin Bayani: Senegal: Jam'iyya mai mulki na kan hanyar samun nasara

Mai-magana da yawun gwamnatin kasar Moustapha Njekk Sarre ya soki kalaman tsohon ministan da aka kora, inda ya ce sojojin da suka taya Faransa yaki lokacin yake-yaken duniya na farko da na biyu sun kasance wadanda kasar take alfahari da su. Tuni mutane a kasar ta Senegal da ke ynakin yammacin Afirka musamman 'ya'ya da jikokin tsaffin sojoji suka fito fili suka tir da kalaman ministan da aka kora.

 


News Source:   DW (dw.com)