Gwamnatin Firaminista Keir Starmer ta kasar Birtaniya ta caccaki matakin korar jami'in diflomasiyyanta daga Rasha, inda ta ce zargin yana leken asiri wannan kage ne da Rasha ta saba kuma wannan ba karon farko ba ke nan.
Karin Bayani: Amurka ta bukaci Rasha da Ukraine zama a teburin sulhu
Mai magana da yawun firamnistan ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa zarge-zargen da Rasha ta yi babu tushe bare makama, kuma Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya saba gabatar da zargin da babu tushe kan jami'an diflomasiyyan da suke aiki a kasarsa. A wannan Talata kasar ta Rasha ta kori wani jami'in diflomasiyyan Birtaniya da take zargi yana leken asiri. Wannan na zuwa lokacin da Rasha take kara takun saka da kasashen Yammacin Duniya kan yakin da take yi a kasar Ukraine.