An kawo karshen kawanyar al-Shabaab a Magadishu

An kawo karshen kawanyar al-Shabaab a Magadishu
Jami'an tsaro a Somaliya, sun kawo karshen kawanyar da mayakan al-Shabaab suka yi wa Otel din nan na birnin Mogadishu na tsawon sa'o'i 30.

Rahotanni na cewa jami'an tsaron na Somaliya sun yi nasarar karkashe maharan tare da kwato dukkanin wadanda suka yi garkuwa da su a gidan saukar bakin wanda ake kira Hayat Hotel.

Akalla dai fararen hula 13 ne suka mutu a harin da al-Shabaab din ta kai da yammacin ranar Juma'a, wasu gommai kuwa suka jikkata.

Da fari maharan na al-Shabaab sun tayar da wasu nakiyoyi ne kafin su kai ga shiga Otel din wanda jami'an gwamnati da 'yan jarida da ma 'yan kasuwa ke zuwa.

An kuma bayyana bukatar kwance boma-boman da maharan suka daddasa a ciki da ma harabar Otel din.

Wannan ne dai hari mafi girma da al-Shabaab din ta kaddamar, tun bayan kama madafun iko da Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya yi cikin watan Yuni.


News Source:   DW (dw.com)