Rundunar Sojin Jamhuriyar Nijar ta ce an kashe mata sojoji 10 a wani harin kwanton bauna da aka yi musu a yankin Tillaberi na yammacin kasar dake kusa da Burkina Faso inda ake yaki da 'yan ta'adda.
Rundunar ta ce wani gungun 'yanbindiga ne ya kaddamar da harin a ranar Litinin a wani sansanin sojin da ke gudanar da bincike kan wasu da ake zargi barayin shanu ne.
Sojoji sun musanta kisan dakarunsu a Nijar
Sojojin sun kara da cewa ba a yi nasarar gano maharan ba a kan lokaci duk da kokarin dakarun sama da na kasa na zakulo 'yanbindigan.Ko da yake sojin sun ce daga baya a ranar Talata sun hango maboyar 'yanbindigan tare da kaddamar da hari kansu lamarin da haddasa mutuwar 15 daga cikinsu.
Sojin Amurka sun kammala ficewa daga Jamhuriyar Nijar
Sojojin da ke mulki sun damke madafun iko a Nijar ne a juyin mulkin watan Yulin 2023, bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum wanda shi ma alokacinsa ya yi ta fama da yakar 'yan'addan.