'Yan sandan Sweden sun ce sun kama mutane a game da kisan wani mutum wanda kafofin yada labarai suka baiyana da cewa Kirista ne dan kasar Iraqi wanda ya yi kaurin suna wajen kona al Qur'ani mai tsarki a shekarar 2023 a Sweden wanda ya haddasa tashin hankali da zanga zanga a kasashen musulmi.
A ranar alhamis ce aka shirya mutumin zai gurfana a gaban kotun gundumar Stockholm domin yanke masa hukunci kan laifukan da ake tuhumarsa na haddasa rikicin kabilanci a kasa.
Mutumin mai shekaru 38 da haihuwa Salwan Momika Kirista ne dan kasar Iraqi da ya sha wulakantawa da kuma kona littafi mai tsarki na musulmi wato al Qur'ani
A yanzu dai kotun ta Stockholm ta dage yanke hukuncin saboda daya daga cikin mutanen da ake tuhuma ya rasu.