Sama da mutum 70 galibin su mata da kananan yara ne wasu 'yan bindiga suka halaka a wasu hare-hare biyu a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.
Hukumomi a kasar sun ce maharan sun afka wa garin Kablangete ne da ke a lardin Ituri inda suka kashe akalla mutum 50.
Haka zalika sun ce wasu daga cikin maharan kungiyar CODECO, sun far wa mazauna kauyen Bikilisende mai tazarar kilomita bakwai inda can ma suka salwantar da sama da mutun 20.
Wasu da suka tsallake rijiya da baya, sun ce maharan sun yi wa mutane ciki har da jarirai yankan rago.
Bayanai na kuma cewa akwai sama da mutun 100 da suka bata a hare-haren biyu.
Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Kwangon, sun ce sun kwashe wasu daga cikin wadanda suka yi matukar jikkata a hare-haren.