Kimanin marasa lafiya 70 ne aka kashe a yayin wani hari da aka kai kan wata cibiyar kiwon lafiya a arewacin Darfur na kasar Sudan. Gwamnan yankin Mini Minnawi ya zargi mayakan kungiyar RSF da kai harin da jirgi maras matuki, inda sukaraunata mutane da dama ciki har da mata da kananan yara.
Hukumar WHO ta bukaci da a dakatar da kaddamar da hare-hare kan cibiyoyin kiwon lafiya, tana mai kira da bangarorin da ke yaki da junada su bayar da damar gyara asibitocin da aka lalata.
Rikici tsakanin rundunar sojin Sudan da mayakan sa-kai na RSF yakaure tun a watan Afrilun 2023, kuma kawo yanzu fito-na-fiton da suke yi ya kashe dubban mutane tare da jefa kusan rabin al'ummar Sudan cikin yunwa.