Kimanin masu taimaka wa sojoji a aikin tabbatar da tsaro 40 ne hade da farar hula aka kashe a wasu hare-hare da aka kai a arewa maso gabashin Burkina Faso.
Harin ya rutsa da 'yan kato da gora da wasu fararan hular a gundumar Guessel da ke a yankin arewaci. Bayan da aka samu saukin hare-hare a tsawon makwanni, a halin yanzu gwamnatin mulkin sojan ta Damiba na fuskantar karuwar hare-haren wanda aka kiesta cewar a kasa da makwanni uku mayakan jihadi sun kashe fararen hula da sojoji sama da dari.
News Source: DW (dw.com)