An kashe dakarun wanzar da zaman lafiya shida a gabashin Dimokuradiyyar Kwango a yankin da sojojin kasar da kuma 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda suke gwabza yaki a ranar Asabar.
Hukumomi sun bayyana cewa an ci gaba da barin wuta a yankin duk da kiraye-kirayen kasashen duniya ga M23 na su dakatar da kutsawa birnin Goma.
Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango za ta yi sulhu da Ruwanda
Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP ya ga hayaki na tashi a wata motar dakarun zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a gefen titi tsakanin biranen Goma da Sake wurin da fada ta kaure a kwananan.
Mai magana da yawun sojin kasar ya ce uku daga cikin sojojin 'yan kasar Malawi ne sai kuma wasu 'yan Afirka ta Kudu uku a cewar wata jam'iyyar siyasar kasar.
Mutane 12 sun mutu a wasu sabbin hare-haren ADF a Kwango
Birnin Goma na da matukar muhimmanci ne saboda albarkatun kasa da ke shimfide a can kuma akwai mutane sama da miliyan daya da ke rayuwa a birnin.
Kungiyar kasashen Afirka ta AU ta bukaci a tsagaita wuta nan take, kamar yadda shugabanta Moussa Faki Mahamat ya bukata tare da kira ga dukkan bangarorin da ke fada da juna su kare fararen hula.