An kammala taron 'yan jaridu na duniya

An kammala taron 'yan jaridu na duniya
Taron 'yan jaridu na duniya kashi na 15 da tasahar DW ke shiryawa a duk shekara ya kammala. An duba batun kalubalen da yan jaridu ke fuskanta a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.

A kalla mutane dubu biyu ne suka hallarci taron na wuni biyu, wanda mafi akasarinsu 'yan jaridu ne daga sassa daban-daban na duniya.

Taron na wannan karon ya yi nazari ne kan halin na tsaka mai wuya da 'yan jarida da ma kafafaen yada labaru suka tsinci kansu a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula kama daga Ukraine da yankin Gabas ta Tsakiya da yankin Sahel na Afirka da kuma arewacin tarayyar Najeriya.

Tashar DW ta mika kyautar fadin albarkacin baki ga 'yan jaridar Ukraine guda biyu domin karrama jarumtarsu wurin fara bayar da rahotannin yadda rikicin Ukraine ya fara ragargaza birnin Mariupol.
 


News Source:   DW (dw.com)