Wani mai magana da yawun rundunar reshen jahar Imo, Michael Abattam, ya sheda ma manema labarai cewa, an kai samame mabuyarsu a ranar Larabar da ta gabata bayan da aka kwarmata masu bincike mabuyar da suka mayar wajen kera bama-baman da suke amfani da su a kai hare-hare a yankin tare kuma da kwace wasu tarin makamai.
Daya daga cikinsu ya taimaka wa bincike wajen amsa laifin kera abubuwan fashewar in ji jami'in. Sai dai a wani martani da kungiyar mai son ballewa daga Najeriyar ta mayar a wannan Asabar, ta nesanta kanta da ma 'yan kungiyar daga batun kera bama-baman da ma hare-haren da gwamnatin Najeriya ta ce, sun yi asarar rayukan mutum sama da dari da talatin daga shekarar da ta gabata.