An kama wadanda ake zargi da sace daliban Greenfield

An kama wadanda ake zargi da sace daliban Greenfield
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu mutane biyu da take zargi da hannu a sace dalibai 20 a kwalejin Greenfield dake jihar Kaduna a shekarar 2021.

Hukumar ‘yan sandan ta kama Aminu Lawal wanda aka fi sani da Kano, da kuma Murtala Dawu wanda aka fi sani da Mugala kan zargin su da hannu a harin da aka kai da makamai a makarantar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani jami'in makarantar. Za'a gurfanar da su a gaban kotu idan 'yan sanda sun kammala bincike.

In ba a manta ba, 'yan bindigar sun saki mutane 14 cikin mutane 20 da suka yi garkuwa da su bayan kwanaki 40 da sace su, sun kashe mutane biyar don tilastawa iyalai da gwamnati biyan kudin fansa.

Yanzu haka dai akwa akalla ‘yan makaranta 1,500 a hannun masu garkuwa da mutane, inda dalibai 16 suka rasa rayukansu, a cewar asusun kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF.

 


News Source:   DW (dw.com)