An kama tan 1.5 na hauren giwaye a DR Congo

An kama tan 1.5 na hauren giwaye a DR Congo
Hukumomi a Kudu maso gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sun kama tan daya da rabi na hauren giwaye a cikin manyan motoci a birnin Lubumbashi.

'Yan sanda sun kama mutane biyar amma biyu sun gudu bayan an yi musu tambayoyi, lauyan kungiyar hadin guiwar kungiyoyin kare muhalli Sabin Mande ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa ya ga buhunan giwaye 18 da aka kama a ofishin mai shigar da kara na jihar da ke Lubumbashi ranar Laraba.

Ana zargin masu safarar hauren giwayen sun yanka adadin giwaye akalla 80 zuwa 100, sai dai haryanzu ba a tabbatar da inda aka fito hauren giwayen ba ko inda za a yi safarar su.

Wannan dai shi ne kame mafi girma a Afirka cikin shekarun baya-bayan nan, bayan da Kenya da Togo sun kama ton hudu na hauren giwaye a 2013 da 2014.

Kasar Sin da kudu maso gabashin Asiya sune manyan kasuwannin hauren giwa na Afirka, wanda akasari ake amfani da su wajen yin maganin da ake zargin a cikin magungunan gargajiya.


News Source:   DW (dw.com)