An kama mai shirin kai hari ofishin jakadan Isra'ila a Jamus

Jami'an tsaro a nan Jamus sun kama wani 'dan kasar Libya da suke zargi da alaka da kungiyar ta'addanci ta IS, wanda ke shirin kai hari ofishin jakadancin Isra'ila da ke birnin Berlin.

Karin bayani:Jamus ta yi kiran a dakatar da rikicin Isra'ila da Hezbollah

Ministar harkokin cikin gida ta Jamus Nancy Faeser ta ce 'yan sanda da sauran jami'an tsaro sun samu nasarar hanzarta dakile nufakarsa, bayan gano musayar bayanai da ya yi da wani 'dan kungiyar IS lokacin da suke tattauna kai harin, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu a birnin Kalsruhe, domin yin ma sa shari'a.

Karin bayani:Jamus ta ba da karin tallafin miliyoyi ga al'ummar Gaza

Nancy Faeser ta ce Jamus ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen kare Yahudawan da ke kasar da ma wuraren da suke.

Kamafanin dillancin labaran Jamus DPA ya rawaito jakadan Isra'ila a Jamus Ron Prosor na godiya ga jami'an tsaron kasar bisa irin kariyar da suke bai wa ofishinsa.


News Source:   DW (dw.com)