An kai kazamin harin ta'addanci a Mali

An kai kazamin harin ta'addanci a Mali
Mutum kimanin 18 aka tabbatar sun mutu a sakamakon wasu jerin hare-haren ta'addanci da mahara suka kaddamar a kan rundunar sojin kasar Mali.

Sojojin Mali goma sha biyar da fararen hula uku ne suka rasa rayukansu a jerin hare-hare da 'yan ta'adda suka kai a kasar Mali. Bayan tabbatar da labarin, rundunar sojin Malin ta ce, ta yi nasarar hallaka mahara akalla arba'in da takwas a yayin gumurzun tare da lalata ababen hawansu. 

Kazamin harin na ranar Larabar da ta gabata, da aka kai kan yankin da ke hada kan iyakar kasar da kasar Mauritaniya, ya kara jefa Mali da ta sha fama da tashe-tashen hankula a yankin Sahel din cikin rudani. Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Bamakon ke kokarin ganin ta tsaya da kafafunta, tun bayan da ta fatattaki rundunar sojin Faransa da suka kwashi shekaru suna taimaka mata yakar ta'addanci. 


News Source:   DW (dw.com)