Kungiyar BLA da ke fafutukar 'yantar da Balochistan ta dauki alhakin harin da aka kai kan karamar bas kusa a jami'ar Karachi, inda ake koyar da harshe da al'adu da adabin Sinanci. 'Yan Chaina uku na daga cikin mutanen da suka mutu a wani harin kunar bakin wake
Dama dai ayyukan da kasar Sin ke gudanarwa sun saba fuskantar kyama a Pakistan, musamman a tsakanin 'yan aware na Balochistan, wadanda suke zargin cewa ana mayar da su saniyar ware a yankin.
Sabon Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi amfani da shafinsa na Twitter wajen yin tir da abin da ya kira "aikin ta'addanci".
Tsaron ma'aikatan Chaina da ke aikin samar da ababen more rayuwa a Pakistan ya dade yana damun birnin Beijing, wadda ta zuba biliyoyin daloli a cikin 'yan shekarun nan