Ministan Harkokin Wajen Chadi Abderaman Koulamallah ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa a halin yanzu dai dakarun sojin kasar sun dakile harin da 'yan bindigar suka yi yunkurin kutsawa fadar shugaban kasar Mahamat Idriss Deby Itno. Wata majiyar tsaro a kasar ta bayyana cewa maharan wani tsagi ne na kungiyar Boko Haram, duk da Ministan Harkokin Wajen Kasar daga bisa ya bayyana maharan a matsayin masu yunkurin tada zaune tsaye da kuma burin hawa madafun iko ko ta halin kaka.
Karin bayani: Chadi ta musanta kashe fararen hula yayin yaki da 'yan ta'adda
Harin na zuwa ne awanni da ganawar da shugaba Mahamat Idriss Deby Itno ya yi da Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi a fadar shugaban kasar. Shugaba Deby na cikin fadarsa a daidai lokacin da 'yan bindigar suka yi ta dauki ba dadi da dakarun sojin kasar.
Karin bayani: Faransa ta fara kwashe sojinta daga Chadi bayan yanke hulda
Kazalika harin na zuwa a kasa da makonni biyu da gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki da na larduna har ma da shugabannin kananan hukumomi da zumar saita kasar kan tafarkin dimokuradiyya duk da cewa 'yan hamayya sun yi fatali da zaben.