An kai hari a wajen bauta a Afghanistan

An kai hari a wajen bauta a Afghanistan
Kafofin sadarwa a Afghanistan, sun ce hare-hare masu kamari sun mamaye wani yanki na Kabul a Afghanistan. Kungiyar IS dai na kai hare-hare a masallatai a kasar.

An wayi da jin karar boma-bomai da ma harbe-harbe a wani wajen bauta da ke a Kabul babban birnin kasar Afghanistan.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gida a gwamnatin Taliban,  Abdul Nafi Takor, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai yi wani karin haske dangane da wadanda suka mutu ko kuma jitta ba kawo i yanzu.

Wasu hotunan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuno hayaki ya turnuke wajen bautan da ake kira gurudwara wanda ke a yankin birnin na Kabul da ma rugugin bindigogi.

Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin kai hari a yankin. Sai dai kuma wani reshen kungiyar IS da ke a Afghanistan din ya sha kai hare-hare a masallatai inda ake da wasu da ake yi wa kallon 'yan tsiraru ne.


News Source:   DW (dw.com)