An jibge dakarun Burundi a gabashin Kwango

An jibge dakarun Burundi a gabashin Kwango
Kasar Burundi ta jibge dakarunta a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ke fama da rikici, domin gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya.

A halin yanzu dai dakarun na sansanin horar da sojoji na yankin Uvira. An dai dorawa dakarun Burundi da kuma takwarorinsu na Kwango alhakin yin farautar dukkannin kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai don dawo da zaman lafiya a gabashin Kwango. Shugaban tawagar sojojin da ke kudancin Kivu Janar Ramanzani Fundi ya bukaci al'umma da su kwantar da hankulansu, tare da bai wa jami'an tsaron hadin kai domin kawo karshen ayyukan bara gurbi. Tun dai a watan Yuni ne shugabannin kasashen yankin gabashin Afirka suka yanke shawarar kafa wata runduna ta yankin da za ta yi aiki tare da sojojin Jamhuriyar Dimukuradiyyar ta Kwango, da nufin murkushe 'yan ta'addan yankin. Alkaluma na nuni da cewa kimanin kungiyoyi masu dauke da makamai 120 ne, ke gudanar da ayyukansu a yankin da ke da arzikin ma'adanai.


News Source:   DW (dw.com)