An ji karar harbe-harben bindigogi a kusa da fadar shugaban kasar Guinea Conakry cikin daren Alhamis, inda kuma sojoji suka yi wa Conakry babban birnin kasar kawanya.
Karin bayani:Hukuncin daurin shekaru 20 wa Dadis Camara
Wani 'dan jarida mai suna Fode Toure da ke kusa da fadar shugaban kasar, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa mutanen garin sun kidime bayan jin amon bindigogin, inda suka rinka guje-guje a dimauce, yayin da su kuma soji ke sintiri a kan tituna dauke da manyan makamai.
Karin bayani:Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya sauka a birnin Conakry na kasar Guinea
Wani jami'in gwamnatin kasar ya shaidawa AP cewa sojojin da suka bude wutar wasu magoya bayan Kanar Celestin Bilivogui ne, wanda aka tsinci gawarsa ranar Laraba bayan kama shi da gwamnati ta yi, kuma tuni aka harbe uku daga cikin sojojin masu bore.