An hallaka minista a Afganistan

An kai hari mafi daukar ran jami'in gwamnatin mafi mukami tun bayan da Taliban ta karbi mulkin Afganistan. A cewar ma'aikatar cikin gida , wani mai kunar bakin wake ne ya kutsa cikin ma'aikatar kula da 'yan gudun hijira, inda nan take bom din da ya fashe ya hallaka ministan kula da 'yan gudun hijira. Khalil Haqqani ministan lura da ayyukan 'yan gudun hijira da aka hallaka, shi ne babban jami'in gwamnati da ayyukan ta'addanci ya yi sanadin mutuwarsu tun bayan da Taliban ta dawo kan mulkin kasar Afganistan shekaru uku da suka gabata. Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin na Kabul.


News Source:   DW (dw.com)