A karshen makon da ya gabata ne mayakan jihadi suka yi dirar mikiya a kauyen da ke kan iyakar kasar da jamhuriyar Nijar, inda akai ta bata kashi tsakaninsu da jami'an tsaro, wanda ya kai ga rasa rayukan jandarma 11 yayin da kusan mayakan jihadi 40 aka kashe har lahira.
A baya-bayan nan ayyukan ta'addanci na kara zafafa a kasar, inda baya ga fararen hula, 'yan ta'addan na yawaitar kai wa jami'an tsaro farmaki.
Kasar ta Burkina Faso ta kwashe sama da shekaru 7 tana fama da ayyukan mayakan da ke gwagwarmaya da makamai wanda ya yi sanadiyar rayukan dubbai tare da raba wasu kusan miliyan biyu da matsugunnensu.