Masu binciken sun ceto mutane 674 a cikin wani kwale-kwalen kamun kifi, jami'an tsaron gabar tekun sun ce wannan samamen daya ne daga cikin jerin ayyukan ceto da suka kaddamar a 'yan kwanakin nan.
Kungiyar agaji ta Jamus mai suna Sea-Watch, ta ceto bakin haure 444 da suke kokarin tsallakawa tekun Bahar Rum a kwale-kwalen 'yan fasa-kwauri, a cewar jami'an agajin, cikin mutane da aka ceto har da mata masu juna biyu da wani mutumin da ya ji rauni na kunar wuta a jikinsa.
Yanzu haka dai bincike ya nuna cewa adadin bakin haure daya bisa uku ne suka shiga kasar Italiya ta barauniyar hanya, idan aka kwatanta da wadan da suka shiga kasar a shekarar 2021.