Kungiyoyin kare hakkin masu sana'ar hakar ma'danan karkashin kasa a Afirka ta Kudu sun yi korafin cewa watanni biyu kenan yanzu da 'yan uwansu sama da 400 ke makale a cikin rami a jigace, tare da tarin gawarwakin wasunsu da suka mutu, sanadiyyar kofar rago da 'yan kasar suka yi musu don jiran dakon cafke su, bisa zarginsu da hakar ma'adanan ba bisa ka'ida ba.
Karin bayani:Jamhuriyar Nijar ta rufe wuraren hakar Gwal mallakin kasar Chaina
Mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin Magnificent Mndebele, ya ce sauran mahakan da ke raye na cikin mawuyacin hali da tagayyara sakamakon yunwa da kuma rashin lafiya da suke fama, a dalilin rashin abinci da ruwan sha.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tabbatar da yin tozali da buhunan da aka kwashe gwarwakin mamatan kusan 50, sai kuma hotunan mahakan da ke nuna yadda suka rame sai kasusuwa ake gani kawai a jikinsu.
Kari bayani:An ceto ma'aikatan ma'adanai a Afirka ta Kudu
Rundunar 'yan sandan Afirka ta Kudu ta sanar da cewa ita ce ta toshe kafofin kai wa mutanen abinci da ruwa domin tilasta musu fitowa don kama su.
Yayiyn da hukumar kula da makamashi da ma'adanai ta kasar ta bakin mai magana da yawunta Makhosonke Buthelezi ke tabbatar da kwashe gawarwakin wadanda suka mutu, amma babu wani karin haske da ya yi, yana mai cewa za su fitar da rahoto nan gaba a hukumance.