A wannan Laraba wata kotu a kasar Tunisiya ta daure jagoran 'yan adawa Rached Ghannouchi shekaru 22 a gidan fursuna wanda shi ne shugaban jam'iyyar Ennahdha mai ra'ayin Islama, bisa zargin cin amanar kasa. Ghannouchi mai shekaru 83 da haihuwa ya kasance tsohon shugaban majalisar dokokin kasar, kuma ya gaba-gaba na masu sukar manufofin gwamnatin Shugaba Kais Saied, wanda ya rikide zuwa dan kama-karya.
Karin Bayani: Martani kan sake zaben Kais Saied a Tunisiya
A shekara ta 2023 aka kama Rached Ghannouchi kuma tun lokacin yake tsare. Haka kotun ta yanke dauren shekaru 35 ga tsohon Firaminista Hichem Mechichi akwai wasu mutanen da aka yanke musu hukunci. Ana zargin gwamnatin kasar ta Tunisiya da ke yankin arewacin Afirka da daukan matakan cin zarafin masu adawa da ita.