An kai wa marbucin nan dan kasar Birtaniya Salman Rushdie hari da wuka a yayin da yake halartar wani taro a yammacin birnin New York na kasar Amirka. Salman Rushdie dai ya shafe tsawon shekaru yana wasan buya, bayan da jagoran juyin-juyin halin Iran Ayatollah Rouhollah Khomeiny ya fitar da fatawar cewa jininsa ya halarta a shekarar 1989, bisa rubutun batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da ya yi.
Wani mahari ne dai ya dabawa Mista Rushdie wuka a wuya a yayin da yake dakon ya gabatar da jawabi a yayin taron na yammcin New York, kana nan take aka garzaya da shi zuwa a asibiti, sai dai ba a yi wani karin haske kan cikakkiyar lafiyarsa ba, sai dai rundunar 'yan sandan Amirka tuni ta tabbatar da kama maharin a wannan yammaci.