An ci gaba da shari'ar jagoran adawa Uganda Kizza Besigye

A Talatar nan ce kotun sojin Uganda ta ci gaba da shari'ar da take yi wa jagoran adawar kasar Kizza Besigye, inda wata hatsaniya ta barke yayin sauraron shari'ar har aka daure daya daga cikin lauyoyinsa.

Karin bayani:Ana tsare da Kizza Besigye a wani sanssanin sojoji

Gwamnatin Uganda na zarginsa da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba da ma wasu laifukan na daban, inda aka kama shi bara a Nairobi babban kasar Kenya, lokacin da yake halartar bikin kaddamar da littafin wata 'yar adawar gwamnatin Kenya mai suna Martha Karua.

Karin bayani:Yuganda: Kotu ta daure Kizza Besigy

A baya dai Kizza Besigye ya kasance babban na hannun daman shugaban Uganda Yoweri Museveni, kuma ma shi ne likitansa, amma daga bisani gayyar ta watse, inda ya rinka shiga takarar zaben neman kada Mr Museveni, amma har yanzu bai samu nasara ba.


News Source:   DW (dw.com)