A wannan Litinin Fiministan kasar Siriya gami da majalisar ministocinsa sun ci gaba da gudanar da ayyuka daga ofisoshin gwamnati a birnin Damuscus, bayan mayakan 'yan tawaye sun kawar da Shugaba Bashar al-Assad wanda ya fice daga kasar. Firaminista Mohammed Ghazi Jalali zai ci gaba da jagorancin gwamnatin zuwa lokacin da za a kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar, kuma ya yi alkawarin ganin harkokin gwamnati sun ci gaba, yayin da 'yan Siriya da ke gudun hijira a kasashen ketere ke neman hanyar komawa gida.
Karin Bayani: Bashar al-Assad na Siriya ya samu mafaka a Rasha
Tuni harkokin rayuwa suka fara komawa sannu a hankali bayan Shugaba Assad ya tsere daga kasar ta Siriya, inda ake kyautata zaton yana kasar Rasha inda ya smau mafakar siyasa. Akwai dai wasu tsaffin manyan jami'an gwamnatin ta Assad da suka tsere. Sannan Firaminista Mohammed Ghazi Jalali ya ce suna aikin kafa gwamnatin rikon-kwaryar cikin tsanaki.
Ita ma kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci samun zaman lafiya na siyasa da kafa gwamnatin da za ta magance matsalolin 'yan kasar gami da sake gina kasar ta Siriya bayan yaki.