A ciki har da wata 'yar majalisar dattawa ta jam'iyyar shugaban kasar da aka yi garkuwa da su wata guda da ya gabata, a mafakar 'yan aware dake a Ashong a arewa maso yammacin kasar wato Elizabeth Regina Mundi tare da kashe wasu mutane 12 da ake zargi da yin garkuwa da su. Wadanda ake kyautata zaton cewar 'yan aware ne na Ambazonia. A ranar 30 ga watan Afrilu ne ‘yan tawayen da ke neman ‘yancin cin gashin kan yankin Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Yamma suka yi garkuwa da Elizabeth.