An ceto daliban jinya 20 a Benue

Wasu kafofin cikin gida a Najeriya sun ruwaito cewa, gwamnati ta yi amfani da wasu jiragen yaki masu saukar ungulu wajen kubutar da daliban, tare da ikirarin kama wasu daga cikin 'yan bindigar.

Masu garkuwan sun dauke daliban na jami'ar Maiduguri da jami'ar Jos tare da likitoci, 'yan bindigar sun kuma nemi a biya su kudin fansa har naira miliyan 50. Najeriya ta jima tana fama da rikicin 'yan bindiga na masu satar mutane don neman kudin fansa.

Wata cibiyar tattara bayanan sirri a Najeriyar, ta kiyasata mutane 4,777 ne 'yan bindiga suka yi garkuwa da su tun hawan shugaban kasar Bola AHmad Tinubu a watan Mayu na shekarar 2023 zuwa watan Agusta na shekarar 2024.


News Source:   DW (dw.com)