Jami'an tsaron sun yi nasarar cafke mutumin dan kasar Iraki da ya kitsa hallaka tsohon shugaban kasar George W. Bush. Mutumin mai suna Shihab Ahmed Shihab da ya nemi mafakar siyasa a Amirka a bara, ya yi yunkurin shigo da wasu 'yan Iraki hudu cikin Amirka ta barauniyar hanya domin taimaka masa aiwatar da shirin kamar yadda binciken Hukumar FBI a kasar ya nunar.
Dan shekaru hamsin da biyu da haihuwan, ya ce, suna son su kashe Bush ne a matsayin fansa a sakamakon umarninsa na mamaye Iraki a shekara 2003 a lokacin da ya ke shugabancin Amirka, lamarin da suka ce, ya janyo asarar rayuka tare da tagayyara kasar ta Iraki.