Taron da zai shafe tsawon kwanaki biyu a na gudanar da shi a birnin Bonn, zai mayar da hankali kan kalubalen da 'yan jarida suke fuskanta a yayin da yake-yake ke kara ta'azara a duniya, kana da ma duba barazanar canjin yanayi, baya ga wasu tarin matsalolin da 'yan jarida ke fuskanta a ko ina cikin duniya.
Batun yakin Ukraine da Rasha na a wasu daga cikin muhimman batutuwan taron, duba da yadda ya janyo gibi da tangarda ga tattalin arikin duniya.
Wannan ne farko shekaru da dama bayan bullar annobar corona, da ake taron da ke zama karo na 15 gaba da gaba, ana kuma shirin karrama wasu 'yan Ukraine biyu da lambar yabo saboda gudummawar da suka bayar ta musamman don sanar da duniya game da gaskiyar haklin da ake ciki a yakin da Rasha ke gwabzawa da Ukraine.