An bude rumfunan zabe mai cike da tarihi a Austria

Mutane miliyan 6.3 daga cikin miliyan tara na al'ummar kasar ne suka cancanci kada kuri'a. Jam'iyyar The Freedom Party (FPOe), da ta shafe shekaru tana mulkin kasar na fuskantar koma baya dangane da yadda matasa ke kauracewa manufofinta da ko da tayi nasara da wuya ta iya kafa gwamnati ba tare da kawancen jam'iyyu ba.

Karin bayani: Kurz ya samu narasa a zaben Austriya 

Jam'iyya mai mulki ta conservative People's Party (OevP) ta shugaban gwamnatin Austria Karl Nehammer, ta sha da kyar a kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a makonnin da suka gabata, inda ta samu kaso 25% bisa 100 na magoya baya.

 


News Source:   DW (dw.com)