An bude rumfunan zabe a Philippines

An bude rumfunan zabe a Philippines
A kasar Philippines al'ummar kasar sun fita zuwa rumfunan zabe domin kada kuri'u a nemawa kasar sabon shugaba da zai jagorance su a wani sabon wa'adin shekaru shida.

 Miliyoyin 'yan kasar tuni suka isa rumfunan zabe domin zaben sabon shugaban kasa da suke fatan ya daidaita al'amuran kasar musamman ma na matsanancin rayuwa da suke fama da shi.


'Yan takara 10 ne ke neman kujerar Shugaba Rodrigo Duterte sai dai karawar ta fi zafi a tsakanin 'yan takara biyu dan tsohon shugaban mulkin kama karya Ferdinand Marcos Junior da kuma abokiyar hamayyrsa Leni Robredo da ke zama mataimakiyar shugaban kasa da ke ci yanzu.

Sama da rumfunan zabe dubu saba'in ne ake sa ran al'ummar kasar za su kada kuri'arsu a yau, kuma ana sa ran rufe su da misalin karfe shidda na yamma.
 


News Source:   DW (dw.com)