Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da wani karin kunshin tallafin makamai na dala miliyan 425 ga Ukraine, wanda yake zuwa a daidai lokacin da kawayen Ukraine ke neman ko ta halin kaka su warware zaren rikicin da ya sarke a tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna.
Fadar White House ta ce a yayin tattaunawar da shugaba Biden ya yi ta wayar tarho da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky ne ya tabbatar da masa da sabon kunshin taimakon, wanda zai ta'allaka musamman ga makaman kare sararin samaniya da tankokin yaki.