Amurka ta fada a ranar Lahadi cewa za ta aika wa Isra'ila garkuwa ta kare makamai masu linzami da kuma sojin kasar a matsayin wani mataki na karfafa mata na'urorin kare makamai masu linzami daga sama biyo bayan harin Iran.
Shugaban na Amurka Joe Biden ya ce zai aika kayayyakin ne domin kare Isra'ila. Mai magana da yawun hukumar tsaro ta Pentagon Pat Ryder ya ce aika garkuwar makamai masu linzami ta THAAD, zai taimaka wa tsaron Isra'ila.
Karin bayani:Netanyahu ya gana da Shugaba Joe Biden a Amurka
Tun da farko a ranar Lahadin, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gargadi Amurka cewa za ta jefa rayukan sojojinta cikin hadari idan ta turasu Isra'ila.
Tun a watan Satumba Isra'ila ta zafafa hare-hare a kan Hezbollah a kudancin Lebanon, baya ga yaki da take yi da kungiyar Hamas ta zirin Gaza.
Karin bayani: Amirka ta gargadi Isra'ila a kan kai hari cibiyoyin man Iran
A yayin da rikicin ke kara zafi sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin da ke Lebanon sun sake bayar da rahoton yadda sojojin Isra'ila ke musu katsalanda a harkokinsu a kasar.
Sojojin sun bayyana cewa a ranar Lahadi tankokin yakin Isra'ila sun kutsa da karfi zuwa cikin sansanin majalisar tare da lalata babbar kofar shigarsa.