Amurka ta karbi sabon jakadan Rasha a Washington bayan sulhu

Amurka ta amince da karbar sabon jakadan Rasha a kasar Alexander Darchiev, bayan mika masa takardar fara aiki a Juma'ar nan a Washington, kamar yadda ma'akatar harkokin wajen Rasha ta sanar.

Karin bayani:Trump ya sassauta matsaya kan hanyar warware yakin Ukraine

A ranar Alhamis Mr Darchiev mai shekaru 64 ya jagoranci jami'an diflomasiyyar Rasha wajen tattaunawa da jami'ar Amurka Sonata Coulter a birnin Istanbul na kasar Turkiyya, domin saisaita alaka tsakanin kasashen biyu.

Karin bayani:Macron na neman shawo kan Trump game da rikicin Ukraine

Sabon jakadan zai maye gurbin Anatoly Antonov da Rashan ta yi wa kiranye a cikin watan Oktoban bara, bayan shafe shekaru bakwai yana aiki a Amurka.


News Source:   DW (dw.com)