Amurka ta janye tallafin da take ba wa Afirka ta Kudu

Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ba za ta katse duk wani tallafin da take ba wa Afirka ta Kudu ciki har da na kudi a wani mataki na nuna adawa da dokar kwace filayen noma da shugaba Cyril Ramaphosa na kasar ya rattabawa hannu.

Trump ya yi barazanar katse zuba Jari a Afirka ta Kudu

Shugaba Trump ya ce Amurka ba za ta taimaka wa gwamnatin Pretoria ba, duba da yadda take ci gaba da take hakin dan Adam,  da kuma yi wa siyasar Amurka ta ketare karan tsaye, inda ya soki zargin Isra'ila da aikata laififukan yakin da Afirka ta Kudun ta yi a baya, da ma huldarta da Iran a wani kudrin da ya sakawa hannu a wannan Jumma'a.

Afirka ta Kudu ta amshi ragamar shugabancin G20

Sai dai tun a gabanin matakin na shugaban Trump ya soma aiki, a wani jawabinsa, shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudun ya ce kasarsa ba za ta kawar da ido ga duk wata barazana ko hurjin mussa ba.


News Source:   DW (dw.com)