Shugaba Biden ya bayyan kwarin gwiwa na cewar kawancensu zai ci gaba da kasancewa a kan gaba wajen samar da zaman lafiya a yankin Indo-Pacific.
Kazalika Biden ya bayyana jin dadinsa ga dorewar dimukradiyya da bin doka da oda, ya kuma jaddada wa al'ummar Koriya ta Kudu Amurka na tare da su.
A ranar Asabar ce majalisar dokokin kasar ta tsige shugaba Yoon daga madafun iko, bayan yunkurin samar da wata dokar soji da ta bar baya da kura a wani mumunan rikicin siyasa da kasar ba ta ga irin shi ba a baya-bayan nan.
Firaminista Han Duck-soo zai ci gaba da zama mukaddashin shugaban kasa har sai kotun tsarin mulki ta kammala hukuncin ta a kan matakin majalisar.
Karin Bayani: Rikicin siyasa ya rincabe a Koriya ta Kudu