Amurka ta bukaci Rasha da Ukraine zama a teburin sulhu

Mike Waltz ya ce lokaci yayi da ya kamata a tabbatar da wanzar da zaman lafiya na dindindin domin dakile asarar rayuka da dukiyoyin al'umma har ma da barazana kan zaman lafiyar nahiyar Turai.

Karin bayani:Amurka za ta ba wa Ukraine tallafin makamai 

A baya bayan nan fadar White House karkashin jagorancin shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden ta bai wa Ukraine umarnin amfani da sabbin makamai masu linzami kirar Amurka domin kai hare-hare kan Rasha, yayin da Moscow ta maida martani ta hanyar amfani da matsakaitan makamai masu linzami masu cin gajeren zango kan Kiev.

Karin bayani:Tsohon shugaban Amurka Trump zai sulhunta Ukraine da Rasha 

Gwamnatin Biden ta jaddada bukatar mika mulki ga sabuwar gwamnatin Trump cikin tsanaki, matakin da shi Trump din ke cewa zai tabbatar da sauye-sauye kan tsaro da diflomasiyyar Amurka da zarar ya hau kan karagar mulkin kasar.

 


News Source:   DW (dw.com)