Wani babban jami'in Amurka ya bukaci bangarorin da ke yaki da juna a Sudan su daina cin zarafin al'umma kamar yadda ake gani a halin yanzu a cikin kasar.
Tom Perriello ya ce sojin Sudan na bitar daftarin kawo karshen yakin a yayin da bangaren mayakan sa kai na RSF suka sanya hannu kansa.
Bukatar isar da agajin gagawa a Sudan
A wannan watan na Agustan 2023 ne mayakan RSF suka amince da batun guje wa cin zarafi bayan Amurka ta shirya wata tattaunawa a birnin Geneva na Switzerland da zummar kawo karshen yakin da ya fi daidaita mutane a duniya.
Cutar kwalara ta sake kunno kai a Sudan mai fama da yaki
Mai shiga tsakani daga kasar ta Amurka a yakin na Sudan Tom Perriello ya kara da cewa Amurka ta gabatar wa bangaren sojinSudan daftarin daina cin zarafi kuma tana jiran amsa, bayan bangaren sojin ya ki bayyana a tattaunawar da aka gudanar a Switzerland.