Amurka ta bukaci kawo karshen yakin Gaza

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi kiran kawo karshen fada tsakanin Israila da kungiyar Hamas da kuma Hizbullah, sai dai luguden wuta ta sama da Israila ke yi kan muhimman wuraren tarihi na Lebanon a birnin Tyre mai tashar jiragen ruwa na nuna babu sassauci a kan haka.

Israila ta fara ruwan bama bamai a kan birnin na Tyre da hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana mai cike da kayan tarihi sa'oi uku bayan sanarwa da ta sanya a yanar Gizo tana umartar jama'a su kaurace wa yankunan. 

Da ma dai dubban jama'a sun fice daga garin na Tyre a yan makonnin da suka gabata yayin da Israila ta zafafa hare hare don tarwatsa Hizbullah a Lebanon da kuma Hamas a Gaza wadanda dukkaninsu ke da alaka da Iran.

Wannan ita ce ziyara ta farko da Blinken ya kai Gabas ta Tsakiya tun bayan da Israila ta kashe shugaban Hamas wanda Amurka ta ce tana fata hakan zai bada damar samun tattaunawar zaman lafiya.

Ana sa ran Blinken zai gana da takwarorinsa na kasashen Larabawa a birnin Londona a ranar Juma'a domin tattauna yakin Israila da Hamas a Gaza da kuma Hizbullah a Lebanon

 

 

 


News Source:   DW (dw.com)