Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta bayyana cewa adadin hukuncin kisa ya sake karuwa a duniya a cikin shekarar da ta gabata. A cikin rahotonta a kan hukuncin kisa na shekarar 2021, Kungiyar ta ce kawo karshen takunkumin corona ya sa an sake komawa gidan jiya, inda ta lissafo akalla hukuncin kisa 579 a cikin kasashe 18 - adadin da ya karu da kashi 5% idan aka kwatanta da shekara ta 2020.
Yawancin kashe-kashen mai yiwuwa sun faru ne a kasar Chaina, in ji Amnesty, duk da cewa gwamnatin kasar na daukar bayanan kisa a matsayin sirrin kasa. Amma kuma Iran ta kasance a sahun gaba wajen aiwatar da hukuncin kisa a kan akalla mutane 314.