Kotun Koli a Amirka ta zartas da hukuncin bai wa jama'a da shekarunsu na mallakar bindiga ya kai, izinin yawo da bindiga don kare kansu sabanin kiraye-kirayen neman an takaita hakkin mallakar bindiga a kasar. Ma'aikatar da ke kula da 'yancin mallakar makamai ta yaba da hukuncin da ya kawo karshen dambarwar da ta barke kan takaita hakkin mallakar makamai a baya-bayan nan a cikin kasar. Kawo yanzu ana da akalla bindigogi miliyan casa'in da ke yawo a hannun Amirkawa.
Dambarwar ta barke a baya-bayan nan a kasar kan takaita amfani da bindiga a sakamakon yawan harbin kan mai uwa da wabi da suka yi sanadiyar salwantar rayuka a sassan kasar. Rahotanni sun gano cewa, an fi samun asarar rayuka ta hanyar amfani da bindigogi a Amirka fiye da rayukan da ke salwanta a tsakanin sojojin kasar da ke a fagen daga koma hatsarin mota da sauran iftala'i.