Amirkawa na iya yawo da bindiga - Kotun koli

Amirkawa na iya yawo da bindiga - Kotun koli
Kotun koli a Amirka ta zartas da hukuncin bai wa jama'a izinin yawo da bindiga don kare kai a sabanin kiran da aka yi na tsaurara dokokin mallakar bindiga.

Kotun Koli a Amirka ta zartas da hukuncin bai wa jama'a da shekarunsu na mallakar bindiga ya kai, izinin yawo da bindiga don kare kansu sabanin kiraye-kirayen neman an takaita hakkin mallakar bindiga a kasar.

Ma'aikatar da ke kula da 'yancin masu mallakar makamai ta yaba da hukuncin da ya kawo karshen dambarwar da ta barke kan takaita hakkin mallakar makamai a baya-bayan nan a cikin kasar. Kawo yanzu ana da akalla bindigogi miliyan casa'in da ke yawo a hannun Amirkawa. Tuni Shugaba Joe Biden ya baiyana takaici kan hukuncin kotun.

Dambarwar ta barke a baya-bayan nan a kasar kan takaita amfani da bindiga a sakamakon yawan harbin kan mai uwa da wabi da suka yi sanadiyar salwantar rayuka a sassan kasar. Rahotanni sun gano cewa, an fi samun asarar rayuka ta hanyar amfani da bindigogi a Amirka fiye da rayukan da ke salwanta a tsakanin sojojin kasar da ke a fagen daga koma hatsarin mota da sauran iftala'i.
 


News Source:   DW (dw.com)