Matakin ya samun amincewar 'yan majalisar Demokrat 223 yayin da 204 suka yi watsi da shi. 'Yan Republican biyar ne suka kada kuri'ar amincewa da matakan, yayin da 'yan Democrat biyu suka kada kuri'ar kin amincewa.
Wakilin Republican Jim Jordan ya ce 'yan Democrat suna tura matakan da ba su dace ba, amma Shugabar majalisar wakilai ta Democrat Nancy Pelosi, ta ce kuri'ar za ta kafa tarihi ta hanyar samun ci gaba. Amma duk da haka majalisar dattijai ne za ta yanke matakin karshe.
Majaalisar ta dauki wannan mataki ne biyo bayan wasu munanan harbe-harbe da aka yi a wata makaranta a jihar Texas, da kuma wani babban kanti a Buffalo d ake binrin New York. A baya-bayan nan ma wani dan bindiga ya kashe mutane hudu a wata cibiyar kula da lafiya da ke Tulsa a Oklahoma.